Shugaban Ƙasa Muhammdu Buhari ya amince da biyan Alawus-Alawus ga Tsaffin Sojoji.
Ƙungiyar Jajirtattun Sojoji dake ƙarƙashin Gamayyar Ƙungiyoyi masu damuwa da Halin Soji sun shiga zanga-zanga a ranar 5 ga watan Janairu tare da gargaɗin lalata bikin ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya da ake yi a ranar 15 ga watan Janairu, amma suka dakatar da zanga-zangar biyo bayan shiga tsakani da Ministan Tsaro Manjo-Janar Bashir Magashi yayi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Soji ta cafke Jami’ai 3 kan saida Harsashi ga Ƴan bindiga
A watan Afrilu, Tsaffin Sojojin sun yi gargaɗin shiga Yajin aikin da suka dakatar, biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya na biyan su haƙƙoƙin su.
Dayake yiwa Ƴan Jarida Jawabi a Abuja a ranar Alhamis, Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro Dr Ibrahim Kana yace Shugaba Buhari ya amince da biyan su alawus nasu.
Yace Shugaban Ƙasa ya amince da kuma gina Sashen Kula da Tsaffin Sojojin a Ma’aikatar.