Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ya ba da sanarwar cewa, ya ba da umarnin cire haramcin da aka sanya wa kamfanin sada zumunta na zama wato Twitter a Nigeria.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan Nigeria, don murnar cikar kasar shekaru 61 da samun yancin kai.
Shugaban, wanda ya amince da shafin Twitter a matsayin dandali mai matukar amfani, ya yi nadamar ce, wasu masu amfani da shafin sun yi amfani da dandalin don yada labaran karya, da kuma inganta tunanin kabilanci da addini.
Ya Kuma ba da umurnin a dage takunkumin da ya sanyawa kamfanin Twitter a Nigeria, amma sai an cika sharuddan da kwamitin shugaban kasa ya gindaya.
KARANTA WANNA LABARIN: Matawalle ya bada Umarnin dawo da Kafofin Sadarwa a Gusau
Buhari ya ce, “Kafofin sada zumunta dandali ne mai matukar amfani wadanda ke baiwa miliyoyin yan Nigeria damar cudanya da masoyan su, inganta harkokin kasuwancin su, zamantakewa da samun labarai da sauran su.
“Koyaya, abubuwan da suka faru kwanan nan sun tabbatar da cewa, dandamalin ba laifuka kawai ake aikatawa aciki ba, ana amfani dashi wajan watsa bayanai ba”
“Don magance wannan mummunan yanayin, Gwamnatin Tarayyar Nigeira ta dakatar da ayyukan Twitter a Nigeria a ranar 5 ga Yuni, shekarar 2021, don ba da damar Gwamnati ta sanya matakan magance wadannan kalubalen” inji shi.
“Bayan dakatar da ayyukan Twitter, Kamfanin Twitter Inc. ya tuntubi Gwamnatin Tarayyar Nigeria, don warware matsalar. Bayan haka, na kafa kwamitin Shugaban kasa don shiga tsakanin bangarorin biyu, domin binciko yiwuwar warware matsalar” a cewar shi.
“Kwamitin, tare da Tawagar Gudanarwarsa, sun yi aiki tare da Twitter kuma, sun magance manyan batutuwa. Waɗannan su ne Tsaron Ƙasa da Haɗin kai; Rajista, Haraji, da sauran su”
“Bayan dumbin ayyukan da aka yi, ana magance batutuwan, kuma na ba da umarnin a dakatar da takunkumin da na sanyawa Twitter, amma sai idan an cika sharuddan, don bai wa yan kasarmu su ci gaba da amfani da dandamali, don kasuwanci da kyakkyawan aiki.”
Buhari ya kara da cewa, Nigeria a matsayinta na kasa, ta kuduri aniyar tabbatar da cewa, kamfanonin sadarwar zamani na amfani da dandalin su don inganta rayuwar yan kasar nan, da mutunta ikon Nigeria da martabar al’adun ta.