• Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sa ke gina sabbin jami’o’in fasaha biyu a Najeriya.
• Ministan ilimi Malam Adamu Adamu, da yasami wakilcin sakataran ma’aikatar ilimi ta kasa ya bayyana hakan a Abuja.
• Ginin jami’o’in zai lashe naira billiyan hudu daga asusun Tetfund.
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, za ta gina wasu sabbin jami’o’in fasaha biyu a jihar Jigawa da Akwa Ibom, sannan za ta inganta wasu jami’o’i 4 da wadatattun kayan aiki.
Ministan ilimi Malam Adamu Adamu, wanda ya sami wakilcin sakataran ma’aikatar ilimi ta kasa Mr Sonny Echono ne, ya bayyana wa mane ma labarai hakan a yau litinin, a babban birnin tarayya Abuja.
Inda ya ce, za a samar da jami’o’in fasahan ne, a jihohin Jigawa da Akwa Ibom.
Kazalika a cewar sa, “Da yuwuwar a samar da kwalejin fasaha ta kasa, wato NIT a garin Abuja, wacce ake saran, zata yi gogayya da ta kwarorin ta, dake kasashen Singapore da Maleshiya”. Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yanke wa wani mai shekara 30, hukuncin zaman gidan yarin na wata 3
Ya kara da cewa, da yuwuwar kammala ginin jami’o’in biyu a cikin wannan shekarar ta 2021, inda gyaran sauran jami’o’in fasahan 4, da kuma kwalejin fasaha ta kasa da za a yi a Abuja, su kammalu a shekarar 2022 me zuwa.
Adumu ya kara da cewa, tuni Shugaban kasa Buhari ya amince da cire naira billiyan 4 na gina sabbin jami’o’in fasahan, daga asusun dake kula da gyaran manyan makarantu wato Tetfund.