Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da naira biliyan 24 ga hukumar kimiya da samar da ababen more rayuwa ta kasa (NASENI) domin gudanar da aikin noman rani na ban ruwa.
Mataimakin shugaban hukumar ta NASENI Farfesa Mohammed Sani Haruna ne ya bayyana hakan a ranar Juma’ar nan bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban a fadar gwamnati da ke Abuja.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban NASENI ya shaidawa manema labarai na fadar gwamnati cewa ya je Villa ne domin ya yi wa shugaban kasa bayanin ayyukan hukumar tare da gabatar da rahoton kudi na hukumar kamar yadda Buhari ya bukata.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/rashin-tsaro-sarkin-bichi-ya-shirya-taron-adduoin-samun-zaman-lafiya-a-jihar-kano/
Ya bayyana cewa hukumar ta fara kera jiragen sama masu saukar angulu a Najeriya, kuma an horas da kwararru kan yadda ake kera jiragen.
A shekarar 2021 ne shugaba Buhari ya amince da ware kashi daya na kason na tarayya ga hukumar NASENI domin gudanar da ayyukan hukumar da samar da injiniyoyi.
(SOLACEBASE)