Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa jami’an tsaro da suyi amfani da Fasahar zamani ta 5G , idan aka kawo ta a ƙasar, domin magance matsalar tsaro a ƙasar.
Shugaban Ƙasar ya bada umarnin a lokacin da yake ƙaddamar da dokar ƙasa akan tsarin 5G domin tattalin arzikin Najeriya a Abuja a ranar Talata.
Buhari yace Gwamnatin Tarayya zata yi kyakkyawan amfani da damar fasahar 5G zata zo dashi a tattalin arziki, tsaro da jindadin ƴan ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tallafin Man Fetur: Janye Aniyar Gwamnati Nasara Ce ga Yan Najeriya— NLC Kano
Ya kuma cire tsoro ga abubuwan da fasahar zata haifar ga ɓangaren lafiya, inda yace an magance wannan matsalar wajen ɓullo da tsarin domin yayi dai-dai da ƙasar.
Akan mahimmancin fasahohin 5G, Shugaban Ƙasar yace zata taimaka ga dukkanin ɓangarori na tattalin arziki, da lafiya, da ilmi, da kuma noma da sauran su.
Buhari ya umarci Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami daya duba yadda za’a ƙaddamar da tsarin, wanda Hukumar Kula da Sadarwa zata yi, tare da goyon bayan wasu Hukumomi na Gwamanti.
Comments 1