A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin halartar taron shugabannin kasashen Turai da na Afirka da kuma shugabannin kungiyoyi da dama a taron kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Afirka karo na shida a birnin Brussels na kasar Belgium.
Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire; Karamar ministar muhalli, Sharon Ikeazor.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo janar Babagana Monguno (Mai ritaya); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar; da kuma babban jami’in hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Hon. Abike Dabiri-Erewa.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce taron da za a yi a ranakun 17 da 18 ga watan Fabrairun 2022 zai tattauna batutuwan da suka shafi duniya a halin yanzu.
Ya ce irin wadannan bangarorin da za a tattauna sun hada da: Bayar da Kudade don Dorewar Ci gaban kasashe masu tasowa,; Canjin yanayi da Makamashi, Zaman Lafiya, Tsaro, sha’anin Mulki; da dai sauran su,
Sauran batutuwan da za a tattauna a cewarsa, su ne; Ilimi, Al’adu da Koyarwar Sana’o’i, Laura zuwa wasu kasashe; Noma da Ci gaba mai dorewa da Tsarin Lafiya da Samar da rigakafin.
Shehu ya ce shugaban kasar zai yi amfani da damar da aka samu wajen yin wasu cudanya tsakanin kasashen duniya.
kazalika Sanarwar, ta ce, Ana Kuma sa ran shugaba Buhari zai dawo kasar nan ne a ranar Asabar Mai zuwa.