By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci zababben shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, da ya kasance mai gaskiya da rikon amana a dukkan harkokinsa.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kogi Ta Gargadi Al’umma Kan Cin Nama Bayan Mutuwar Shanu 20 A Jihar
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin Adamu da tsohon shugaban kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC mai rikon kwarya da kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a fadar gwamnati da ke Abuja.
Shugaba Buhari ya bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan kasar za su ci gaba da marawa APC baya a yakin neman zabe.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya tabbatar wa jam’iyyar da kuma al’ummar kasar cewa zai ci gaba da fafutukar dora ka’idojin dimokaradiyya a cikin harkokin siyasa da kuma harkokin mulki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A yau ya kamata mu yi farin ciki da cewa jam’iyyar ta yi jinyar raunukan da ta samu, ta kuma warkar da kanta yadda ya kamata, don yin tattaki domin tunkarar kalubalen zaben jahohi da na kasa baki daya.
“Lokacin da na yi tunani a kan manufofin gwamnati a kan tattalin arziki da kuma musamman a fannin bunkasa noma, samar da ababen more rayuwa, ICT da kirkire-kirkire da kuma matakan jin dadin da muka sanya wa mata, matasa da marasa galihu a cikin al’umma.
Kazalika yace na yi la’akari da manufofin gwamnati kan tattalin arziki, mu kara kwarin gwiwa cewa ’yan kasarmu za su ci gaba da marawa APC baya a yakin zabenmu.”
Comments 1