Kungiyar Kare Hakkin Musulmai ta MURIC ta ce lura da yadda matsalar man fetur ke kamari a Birtaniya ya kamata a ce ‘yan Najeriya sun gode wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
MURIC ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta fitar, wanda Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya ce a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari ba a rika fuskantar dogayen layuka a gidajen mai ba.
Kusan makonni biyu ke nan ana samun dogayen layuka a gidajen mai a Birtaniya.
Kuma rahotanni sun nuna cewa gidajen mai 5,500 daga cikin 8,000 ba su da man kwata-kwata.
Lamarin ya sa Firanminista Boris Johnson ya ce gwamnatinsa za ta ba da biza ga direbobin tankokin mai 5,000 daga kasashen waje don su yi aikin dakon mai a kasar.
A cewar Farfesa Akintola “karancin man fetur a Birtaniya ya haifar da karancin abinci da turmutsitsi a gidajen mai.