Shugaban kasa Buhari ya bada umurnin a biya Malaman Jami’ar da ba sa tsarin IPPIS albashinsu na watannin Fabarairu da Maris da aka rike.
Ministan Kwadago, Dr Chris Ngige shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai tallafa masa kan kafafen watsa labarai, Emmanuel Nzomiwu a ranar Talata.
Ngige ya ce shugaban kasar ya bai wa ministar kudi da tsare-tsare da kuma ofishin Akanta Janar na gwamnatin tarayya umurni da su yi maza su biya su albashinsu domin saukaka musu radadin zaman gida da suke yi da su da iyalansu saboda Koronabairos.
Ministan ya ce an nemi shugabannin Jami’a da su aika da sunayen Malaman Jami’ar da abin ya shafa ofishin AGF domin ganin an biya su.