A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana daban-daban da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da takwaransa na jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja.
Tambuwal, wanda shi ne Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, na daya daga cikin manyan masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa a zaben badi.
Bagudu shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar (PGF), dandalin da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki ke amfani da shi.
Ziyarar da gwamnan jihar Sokoto ya kai wa shugaban kasar ta zo ne kwanaki kadan bayan da jam’iyyar PDP ta samu daidaito a tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa hudu na arewa.
Sai dai wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasar sun ce shugaban ya gayyaci wasu gwamnonin jihohinsu ne kawai Saboda suna da iyaka da kasashen da ke makwabtaka da kasar nan.
A wani labarin Kuma na daban.
A yammacin yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin shugaban jam’iyyar APC mai mulki a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Gayyatar dai na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da aka rabawa manema labarai a fadar shugaban kasa, wadda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Afrilu, 2023.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron akwai tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, tsoffin shugabannin jam’iyyar APC na kasa, Dakta John Oyegun da Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba.
Sauran sun hada da shugaban riko na farko na jam’iyyar APC, Bisi Akande, tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu-Sheriff, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Yarima, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamako, tsohon gwamnan jihar Edo, Oserheimen Osunbor, tsohon Gwamnan jihar Yobe Bukar Ibrahim, Janar Muhammed Magoro, Sanata Lawal Shuaibu, Aba Aji, Tijjani Tumsah, Fati Bala, Abubakar Guru da Nasiru Danu.
Ina mai sanar daku cewa Shugaban kasa ya ba da umarnin a mika gayyata zuwa ga jerin sunayen shugabannin jam’iyyar APC domin su hada kai da shugaban kasa domin buda baki a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, 2022, da karfe 18:30 a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Gidan Gwamnatin birnin tarayya Abuja.
Dangane da haka, ana roƙon ka da ka gayyace su su halarta. Shugabannin za su isa kofar wajen da karfe 16:30 don gwajin gaggawa na Covid-19 a Cibiyar Taro na Gidan Jiha kuma a zauna a wurin da karfe 18:00, “in ji sanarwar.