Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin duniya game da ambaliyar ruwan data afku a kasar Pakistan.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya jajantawa yadda ambaliyar ruwan teku ta bayyana a matsayin bala’i mafi muni a tarihin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Buhari Ta Tallafawa Wata Jiha Da Kayan Abinci
Dan Takarar Shugaban Kasa A NNPP, Kwankwaso Ya Bude Sakatariyar Jam’iyyar A Borno
Ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje rabin miliyan, ta shafi mutane kusan miliyan 30, sannan ta kashe sama da 1,000, ta kwashe daruruwan tituna, gadoji da sauran ababen more rayuwa.
Shugaba Buhari ya ce Pakistan da al’ummarta na cikin tunani da addu’o’in ‘yan Najeriya yayin da suke fuskantar wannan bala’i na jin kai.
Ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran Hukumomin agaji da su dauki matakan gaggawa don taimakawa mutanen da ba su da matsuguni da abinci da kuma miliyoyin da ke bukatar agajin gaggawa.
A wani labarin kuma Gwamna Buni Na Murnar Cikar Jihar Yobe Shekaru 31, Ya Jinjinawa Shugabannin Da Suka Shude
Gwamna Mai Mala Buni ya taya al’ummar Yobe murnar cika shekaru 31 da kafuwar jihar.
Buni a cikin wata sanarwa ta hannun babban daraktan yada labaran sa da hulda da manema labarai, Alhaji Mamman Mohammed ranar Asabar a Damaturu, ya yabawa magabatansa bisa gudunmawar da suka bayar wajen dora jihar a kan turbar zaman lafiya da ci gaba.