Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya jajanta rasuwar fitaccen ɗan kasuwar Kano Alhaji Shehu Rabi’u wanda ɗan uwa ga marigayi Isyaka Rabi’u.
Shugaba Buhari ya turo da saƙon gaisuwar ne ta hanyar hadiminsa Malam Garba Shehu, a ranar Asabar.
https://dimokuradiyya.com.ng/pdp-ta-yi-taaziyyar-rasuwar-isa-funtuwa/
A saƙon ya tura jajensa ga iyalan Isyaka Rabi’u da kuma Abdussamad Rabi’u wanda shi ne shugaban kamfanin BUA, shugaba Buhari ya bayyana mamacin a matsayin jagoran da kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasar nan.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Buhari ya kuma jajantawa Masaurata kuma dukkain ilahirin jama’ar Kano bisa wannan babban rashi da aka yi.