Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau, ya gabatar da tutar APC ga sabon shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara,, Gwamna Bello Mohammed Matawalle MON (Shattiman Sakkwato), a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Wannan sanarwar yana dauke ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Darakta Janar kan harkar yada labaru da Fadakarwa da Sadarwa na Gidan Gwamnati, Alh Yusuf Idris Gusau.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hannunta Tutar Jam’iyar APC ga Gwamnan Jihar Zamfara, Alh. (Dr.) Bello Mohammed (Matawallen Maradun) don jan ragamar Jam’iyar ta APC a jihar.
Bukin mika tutar Jam’iyar APC ga Gwamna Bello Mohammed ,wanda a ka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, ya tabbatar wa duniya cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Uwar Jam’iyar APC sun amince da wannan Jagoranci na Matawalle.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindigan sun saki Sarkin Kajuru
An roki Allah (SWT) Ya sa wannan lamari ya zama sanadin samun cikakken tsaro da zaman lafiya, da inganta Ilmi da Noma da Kasuwanci, da kuma samun karuwan arziki .
Gwamnan Matawalle wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, daga PDP a ranar 29 ga watan Yuni, ya na tare da takwaran sa na jihar, Cross Rivers, Ben Ayade
Gwamna Matawalle tuni ya koma APC ne tare da dukkan mambobin majalisar dokokin jihar ta Zamfara, da dukkan sanatocin uku daga jihar, da kuma shida daga cikin ‘yan majalisar wakilai bakwai dake jihar.