By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban hukumar NNPC tare da Mele Kolo Kyari da Umar I. Ajiya a matsayin Babban Darakta, da Babban Jami’in kula da sha’anin Kudi.
Shugaban ya ba da umarnin hada kamfanin na NNPC Limited daidai da tanadin dokar masana’antar man fetur PIA.
“Don haka, an umarci Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC, Mista Mele Kolo Kyari da ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da shigar da NNPC Limited yayi daidai da tanade tanaden PIA 2021.
“Hakanan, kundin tsarin mulki ya bashi iko a karkashin sashi na 59 (2) na PIA 2021, Shugaba Buhari ya amince da nadin Kwamitin Gudanar da Kamfanin NNPC Limited, daga ranar da aka kafa Kamfanin.
“kazalika Shugaban Hukumar shine Sanata Ifeanyi Ararume, yayin da Mele Kolo Kyari da Umar I. Ajiya sune Babban Darakta, kuma Babban Jami’in Kudi.
“Sauran Membobin Hukumar sune Dakta Tajudeen Umar Arewa maso Gabas, Misis Lami O. Ahmed Arewa ta Tsakiya, Mallam Mohammed Lawal Arewa maso Yamma, Sanata Margaret Chuba Okadigbo Kudu maso Gabas, Barista Constance Harry Marshal Kudu maso Kudu, da Cif Pius Akinyelure Kudu maso Kudu ”