By Muhammad A. Dalhat
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Armaya’u Bichi a matsayin sabon shugaban Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsin-Ma a jihar Katsina.
Hakan na dauke ne a wata sanarwa da ministan ilimi, Adamu Adamu ya sanyawa hannu kuma Jaridar Madubi ta ga takardar sanarwa. Wanda nadin shi a matsayin shugaban Jami’ar zai fara daga 15 ga watan Mayun 2015.
Adamu Adamu ya ce; nadin na shi wa’adin mulki guda ne har na tsawon shekara biyar. Inda ya ce shugaban Jami’ar zai samu dukkanin abin da doka ta tanadarwa dukkan wani shugaban Jami’a.
A karshe ya taya shi murnar kammala wa’adin mulkinsa cikin kyakkyawan nasara.
Farfesa Bichi ya taba rike Jami’ar har na tsawon fiye da shekara biyu a matsayin mukaddashin shugaban Jami’ar kafin daga bisani aka cire shi.