Jaridar TVCNEWS ta ruwaito Shugaba Buhari ya zabi sabbin sakatarori guda biyar na gwamnatin tarayya.
Shugaba Buhari ya aminci da daukan sabbin sakatarori guda biyar wadanda zasu cigaba da aiki a gwamnatin tarayya.
Yannan ya biyo bayan kammala daukan sabbin sakatarori na dindindin cikin maaikatan tarayya.
KARANTA:- Ina samun dubu 400,000 a duk wata, WANI Matashi Mai sayarwa barayi biredi
Dr. Folasade Yemi Esan shugaban ma’aikatan tarayya ya bayyana hakan cikin bayanin Mai kula da huldan jama’a AbdulQaniyu Aminu, a Abuja.
Sunayen Ma’aikatan da aka dauka sun hada da Mr. Adebisi Okufanju (Ekiti), Mrs Maryann Owundiwe (Enugu State), Mr. Yusuf Ibrahim (Katsina State), Mr. Ogunbiyi Olaniyi (Lagos State) da Ibrahim Kana (Nasarawa State).
Yemi Esan yace nan da bada jimawa ba wadanda aka zaba za’a kaddamar dasu domin cigaba da aiki.
A WANI LABARIN:- Gwamanan dai Jim kadan bayan aukuwar lamarin ya bayarda umarnin daukan matakin gaggawa don ganin an kubutar da daliban da Malaman.
Anyi musayar wuta tsakanin sojojin da Yan bindigar lokacin da ake kokarin kubutar da daliban.
A lokacin da ake kokarin kubutar da daliban da Malaman anyi arangama da barayin bayan da jami’an tsaro suka fatattako su tun daga yawuri zuwa Riyao zuwa garin Samba, a lokacin ne Yan bindiga suka rabu gida biyu wasu suna kora daliban da Malaman wasu Kuma suna kora sharu.
Nwachuku ya bayyana cewar ” sojojin kasa gami da na sama ne sukai gamin gambiza wajan kwato rayan inda suka farama yan bindigan Aman wuta misalin karfe 2:30.
A lokacin, sojojin sun dawo da shanu kimanin 800 inda suka ce zasu cigaba da bin diddigin Yan bindigan har sai sunje inda suke Tara mutane don kwato su.
Sojan yace za’a damka daliban da Malaman wajan Gwamnatin Jihar kebbin
Gwamanan Jahar kebbin ya bayyana dawowar daliban ne a yammacin yau Juma’a inda jami’an tsaro suka dawo dasu.
Comments 1