• George Abang Ekpungu shi ne sabon sakataran hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC.
• Wasu mutun hudu da su ka fito daga sassa daban da daban na kasar nan ne su ka yi nasaran kasan cewa, sabbin mambobin.
• “Munyi nadin ne bisa bin kundun dokar hukumar EFCC.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada George Abang Ekpungu a matsayin sakataran hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC
Dr Umar Gwandu wanda shi ne baban mai taimaka wa Ministan Shari’a na kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a ne, ya tabbatar da nadin a yau litinin, a baban birnin tarayya Abuja.
Inda ya ce, sabon na din zai yi zai yi aiki ne, har nan da shekaru biyar masu zuwa a nan gaba.
Ya Kuma nada mambobin gudanar wa, da su ka hada da; Luqman Muhammad daga yankin Kudu maso Kudu, Anumba Adaeze daga Kudu maso Arewa, Alhaji Kola Raheem Adesina daga yankin Arewa ta Tsakiya, da kuma Alhaji Yahya Muhammad daga yankin Arewa maso Gabas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe wani mutun bayan ya ciru makudan kudaden a ATM
Gwandu ya kuma ce, nadin ya zo dai dai da sashin doka na 2 daya cikin baka, da kuma sashi doka na 4, na aikin hukumar ta EFCC na shekarar 2004.
Ya ce, hukumar ta EFCC ta dade ta na gudanar da aikin ta, ba tare da wasu mukamai ba, tun shekarar 2015.
Kazalika, “Tuni Buhari ya bada umarnin tura sunayen mutanan zuwa majalissar dattijan kasar nan domin tabbatar wa” Inji NAN.