Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mohammad Shehu a matsayin Sakataren hukumar Haraji ta RMAFC wanda zai kwashe shekara biyar da wannan mukamin.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin SGF din, Willie Bassey ya fitar a Abuja.
Shugaban kasa Buhari har wala yau ya nada Bitrus Chinoko a matsayin Babban Daraktan CMD, reshen Legas, wanda aikinsa ya fara daga 27 ga watan Afrilu.
Kafin bai wa Chinoko wannan mukamin, shi ne ke rike da mukamin a matsayin mukaddashi. Shugaban kasar ya taya su murna bisa wannan mukamin da aka nada su, inda ya shawarce su da su yi amfani da basirar da suke dashi wajen sauke nauyin da aka dora musu.