Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi hadin kan shugaban Rasha, Vladimir Putin domin ya taimaka masa ta bangaren soji wajen kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram arewa maso gabashin Nijeriya.
Rahoto daga kafar watsa labaran Rasha ta Kremlin’s RIA, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya labarto, an bayyana cewa; shugaban kasa Buhari zai sanya hannu a wata yarjejeniya da kasar Rasha a birnin Sochi na kasar kafin karshen watan Oktoba.
Jakadan Nijeriya a Rasha, Stephen Ogbah ya bayyana cewa; yana da kwarin guiwa Nijeriya za ta kawo karshen Boko Haram idan har Rasha ta amince za ta tallafawa Nijeriya wajen kawo karshen Boko Haram din musamman idan aka yi duba da kwarewarsu wajen yakar ‘yan ta’adda a Siriya.
A cikin shekarar 2018 Nijeirya ta siya wadansu jiragen yaki guda biyu kirar Tucano daga kasar Amurka, wanda ake sa ran jiragen yaki za a kawo su a cikin shekarar 2020.
A cewar Ogbah, Nijeriya tana sha’awar siyen tankokin yaki da jiragen yaki da sauran kayayyakin yaki na soji daga kasar Rasha, inda ya ce; tuni ma aka rubuta bukatar hakan.