Buhari ya roƙi Al’ummar Neja Delta dasu bashi dama ya Shimfiɗa Ayyuka a yankin su
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya buƙaci Al’ummar Neja Delta da su kasance masu kamun kai tare da ba da damammaki wajen aiwatar da ayyukan cigaba da shirye-shiryen gwamnati da dama da aka fara yi wa yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za Mu Sauƙaƙa rayuwar Alƙalai a Najeriya – Shugaba Buhari
Ya yi wannan jawabi ne a wajen bude taron kwana biyu da Ma’aikatar Harkokin Neja Delta ta shirya wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Buhari, wanda Ministan Sufuri, Muazu Sambo ya wakilta, ya ce aikin titin yankin Gabas maso Yamma da ke gudana ya kasance ɗaya daga cikin manyan ababen more rayuwa a Najeriya, da kuma wajen hada manyan biranen kasar nan da suka fi hada-hadar kasuwanci a yankin.
Ya ce za a kammala aikin kafin ƙarshen wa’adin mulkin sa a shekara mai zuwa.
Ya umurci Kamfanin mai na Nigeria National Petroleum Company Limited da sauran rassansa da su gyara sashe na 4 na titin yankin Gabas ta Yamma (Eleme Roundabout zuwa Onne junction) ta hanyar tsarin biyan haraji.
Buhari ya yi tsokaci kan shirin gwamnati na kafa sabuwar hukumar raya yankin Neja Delta (NNDC).
Ya umarci Babban Sakatare a ma’aikatar harkokin Neja-Delta ya gudanar da aikin tantance ma’aikatan hukumar ta NNDC domin samar da ma’aikata da suka dace da kuma sanya ma’aikatan da suka dace.