Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, a karshen mako ta kammala rabon kayan abinci ga ‘yan gudun hijira kimanin 149,448, wadanda ke zaune a sansanoni 18, wadanda aka kwato na mazauna jihar Borno.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NEMA Manzo Ezekiel ya fitar, ta ce an raba tallafin ne domin tunawa da ranar jin kai ta duniya, inda ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin ne a garin Maiduguri na jihar Borno, kuma ya kaddamar da kayan agajin da hukumar NEMA ta kai domin ci gaba da rabawa ‘yan gudun hijirar.
Karanta kuma: Buhari ya isa Maiduguri, ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da Gwamnatin Jahar tayi
Sanarwar ta ce, kayayyakin sun hada da abinci da wanda ba kayan abinci ba, wadanda suka hada da, buhunan shinkafa 24, 908; buhunan wake 24,908 da buhunan masara 24,908. Har ila yau, rabon ya haɗa da katun 2,409 na kayan magi; 2,075 kwali na tumatir gwangwani; 1 245 na gishiri da kuma 2,409 na kayan lambu.
Sanarwar ta kara da cewa: “Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, a madadin gwamnatin tarayya, tana baiwa ‘yan gudun hijirar kayayyakin abinci na wata-wata a sansanonin, da masu masaukin baki da kuma al’ummomin da aka kwato Sansanoninsu da suka hadar da Madinatu, Muna Garage, Goni Kachala, Gidan Kwastam da Shuwari Ngom a Maiduguri. Al’ummomin da suka karbi bakuncin sun hada da Kusheri, Polo St. Hillary, New Prison, Suleimanti, El-Yakub, Filin Ball, Bulabulin Ngarnam Khurso Bashar da Wagami. Al’ummomin da aka ‘yantar sun hada da Benisheik, Mainok da Jakana,” jaridar Vanguard ce ta rawaito labarin.
A wani labarin da ban: Karo Na Uku, Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Maiduguri
Shirye shirye tuni sun kammala zuwa Yanzu, domin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin Maiduguri.
Jaridar Dimokuraɗiyya ya rawaito cewa ziyarar ita ce ziyarar aiki ta uku da shugaban ya kai Maiduguri cikin shekara guda, bayan wadda ya kai ta 17 ga watan Yuni da 23 ga Disamba a shekarar 2021.