Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya isa birnin London, don ganin likita domin duba lafiyarsa, sannan zai halarci wani babban taro da za’a gudanar kan Ilimi tare da hada hannu wajan habbaka Ilimi daga shekarar 2021 zuwa 2025. Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Jirgin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dira a birnin London da misalin karfe sha daya da minti ashirin da biyar agogon Najeriya, inda yanayin garin na daidai da ashirin da biyu na ma’aunin salshas.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya sanar, yace taron wanda Ministan Birtaniya Boris Johnson, zai gabatar shida shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta.
KARANTA:- Shugaba Buhari ya sanya hannu kan ƙarin kasafin kudin 2021
Kamar yadda yace wannan taro zai kara karfafa kawance tsakanin kasashen, tare da tallafawa matasa dake kasashen, hakan kuma zai bada damar kawo sauyi don cigaban harkokin Ilimi a Kasashen.
“Taron zai taimakawa shuwagabanni wajan tallafawa harkokin Ilimi a Kasashe casa’in a wannan duniya har na tsawon shekaru biyar.”
Femi Adesina, ya kara da cewa “Taron dai zai kunshi tattaunawa akan Muhimmancin Ilimi, Musayar fasahohin gabatar da Ilimi a tsakanin kasashen, Samar da sauye-sauye don tallafawa karatun Mata, bada tallafin kudade don bunkasa ilimi har na tsawon shekaru biyar. Wadanan na daga cikin abubuwan da za’a tattauna akansu yayin gudanar da taron kamar yadda ya zayyana
Sannan shuwagabanni Najeriya za suyi taro na musamman dan Ministan Birtaniya Boris Johnson.
Femi Adesina, yace bayan sun kammala taron, shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai shafe Yan kwanaki kadan don duba lafiyarsa.
Ana sa ran shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya a sati na biyu cikin watan Agusta mai kamawa.