Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa birnin Madrid na kasar Spain domin ziyarar aiki bisa gayyatar da shugaban kasar Spain, Pedro Sanchez ya yi masa.
Shugaba Buhari ya tafi ne tare da rakiyar ministan yada labarai da raya al’adu, Alhaji Lai Mohammed; Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; Ministan matasa da wasanni Sunday Dare da karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora.
Kakakin shugaban kasar, Mista Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
A cewar Adesina, a wata ganawa ta daban a yayin ziyarar, shugaba Buhari zai gana da uban kasar Spain, mai martaba Sarki Felipe VI.
Mai taimaka wa shugaban kasar ya bayyana cewa shugaban zai kuma kasance babban bako na musamman a wani taron zuba jari da kungiyar ‘yan kasuwa ta Spain, da ma’aikatar kasuwanci, da kuma kungiyar masu daukan ma’aikata suka shirya.
Shugaban na Najeriyar zai yi jawabi ne ga taron manyan ‘yan kasuwar kasar Spain da takwarorinsu na Najeriya kan damar zuba jari a Najeriya da hanyoyin fadada yawan kasuwanci tare da kara yin hadin gwiwa don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.
Adesina ya ce Buhari zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo.
Sauran da ke cikin tawagar shugaban sun hada da; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno mai ritaya; Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i; Haka kuma shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa suna cikin tawagar shugaban kasar.
Comments 1