Jiya Alhamis, ya tashi daraf yayi lulaye zuwa Ingila. Kamar yadda Femi Adeshina kakinsa ya bayyana, Baba Buharin zai je Ingila ne, ya lafe a wani sansanyar wuri.
Buharin, ya wanke kafarsa ya bar Najeriya ne, a dai dai lokacin da mahara suka kai hare hare a Jihar Katsina, jiharsa ta haihuwa. Har dubbai suka watse, babu inda za su kwana.
A dai dai lokacin da Najeriya ke fuskantar ma fi munin rashin tsaro da talauci da ba a taba fuskantar irinsa ba.
To, wai shin Baba Buhari, duk niímar da ke cikin Villa sun yi maka kadan da za ka zauna ka yi nazari, sai ka kwashi miliyoyin talakwan da suka zabe ka, ka tafi Ingila ka kwanta?
Allah ya sa dai Shugaban EFCC, yana biye da kai.