Rahotannin dake fitowa daga Saudiyya, sun bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bar garin Makkah zuwa birnin Jeddah da misalin karfe 1:30 na yamma agogon can, inda jirginsa ya nufi Landan da misalin karfe 3:05.
A ranar Alhamis din nan ne, Yariman Saudiyya, Mohammed Bin Salman ya kai wa shugaban kasar ziyara a Otel din Ritz Carlton, inda suka yi wata ganawar sirri ta musamman a tsakaninsu.
A yayin zaman, Yariman ya yi kira ga hadin guiwa na musamman tsakanin Nijeriya da Saudiyya wanda hadin guiwar zai bunqasa cinikayya da kuma hulda a tsakanin kasashen.
Magajin garin Jeddah, Almeer bin Abdallah bin Jalawi shi ne ya yiwa shugaban rakiya zuwa filin jirgin a yau. Kuma ana sa ran shugaban kasar zai kwashe mako biyu a birnin Landan.
Tafiyar na shugaban kasa na zuwa ne bayan ya kammala Umurah jim kadan da kammala taro kan huldar kasuwanci da ya gudana a garin Riyadh daga 29-31 ga watan Oktoba.
A yayin kasancewarsa a birnin Riyadh, shugaban kasar ya gana da Sarkin Saudiyya, Salman, inda shugabannin suka jaddada bukatar kulla alaka ta dindindin tsakanin Nijeriya da Saudiyya musamman a bangaren iskar gas da man fetur.