A yau Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya taya mataimakin sa Yemi Osibanjo muranar zagayowar ranar haihuwar karo na 66. Kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Shugaban kasar ya yaba wa Osibanjo kan yadda ya haɗa wasu ayyukah da gudanar da sha’anin mulki.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Mummunan Zanga-Zanga Ta Barke A Jojiya
Shugaban, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar, ya taya daukacin iyalan Osinbajo murnar zagayowar ranar haihuwar Dan nasu, mijinsu kuma mahaifinsu bisa sake samun ƙarin shekara guda, cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Da yake yiwa mataimakin shugaban kasa da iyalansa fatan alheri, shugaba Buhari ya yaba da irin gagarumin hidimar da Osibanjo yayi wa kasar nan, a matsayinsa na malami, babban lauyan gwamnatin jihar Legas a tsakanin shekarrun (1997-2007), kuma mataimakin shugaban kasa a tsakanin shekarar (2015 har zuwa yau).
A wani labarin kuma, Zaben Gwamna: Ku tabbatar da dai-daito, kar a nuna son zuciya– PDP ta fadawa INEC
Wakilin Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Danjuma Bello Sarki ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da ta tabbatar da daidaito da kuma nisantar kanta daga son zuciya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sarki ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu an samu i korafe-korafe daban-daban daga zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gabata, inda ya bukaci a gyara kura-kurai da aka gano kafin zabe mai zuwa.