Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya zuwa Afirka ta Kudu tare da wasu Gwamnonin jihohin Kano da Filato wato Abdullahi Ganduje da kuma Simon Lalong a ranar Laraba.
Shugaban kasar ta hannun Kakakinsa, Garba Shehu ya taya Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Plateau Simon Lalong murnar nasarar da suka samu a kotun sauraron kararrakin zabe.