Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin gargajiya na Okori Eleme, Egbere Emere Okori Eleme murnar cikar shekararsa 50 a duniya a ranar 15 ga watan Janairun 2020.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja, inda shugaban kasa Buhari ya aika da sakon taya murna ga Sarkin mai daraja ta daya na jihar Ribas a ranar 30 ga watan Disamban 2019.
A takardar shugaba Buhari ya taya Sarkin da masarautar baki daya bisa cika Sarkin shekara 50 a duniya. Inda Buhari ya jaddada taya murnarsa ga masarautar Okori Eleme da al’ummar jihar Ribas bisa nasarorin da suke samu dangane da tallafawa al’umma da kawo ci gaba.
A karshe ya yi masa addu’ar kariya ta musamman da kuma masarautar.