Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya taya shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Brig.Janar Buba Marwa (mai ritaya),murna a kan nasarar da hukumar ta samu a baya-bayan nan da ya kai ga farfasa wata kungiyar dillalan kwayoyi ta kasa da kasa tare da kwato kilogiram 1,855 na hodar iblis.
Hakan na kushe ne ta cikin wata wayar tarho da ya yi da shugaban hukumar yaki da muggan kwayoyi daga birnin New York inda yake halartar taron majalissar dinkin duniya karo na 77 (UNGA 77), shugaba Buhari ya ce labarin kame kayan ya faranta ran sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nada Ni A Matsayin Ko-odinetan Matasa Na Yakin Neman Zaben Tinubu Abin Mamaki Ne – Yahaya Bello
“Ina matukar godiya da aikin da kuka bayar wajen kawar da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi. Ya faranta min rai yayin da nake ci gaba da bin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin ku.”
“Kun nuna sau da yawa cewa zabar ku don jagorantar wannan yaƙin da miyagu ƴan kasuwan mutuwa waɗanda kawai manufarsu ita ce yi wa matasanmu barazana da kuma dagula makomar matasanmu, zaɓi ne mai kyau, Da fatan za a ci gaba da aikin.”
A wata ganawa da ya yi da ‘yan tawagarsa daga baya, shugaban ya ce, “Buba Marwa yana cikin koshin lafiya. Ton biyu na hodar iblis, shi ne ja.”
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Hukumar NDLEA ta cafke hodar iblis da ta kai kimanin dalar Amurka miliyan $278,250,000 dai dai da naira Biliyan 194 a kudin Najeriya tare da kama barayin miyagun kwayoyi ciki har da wani dan kasar waje a wani babban samame da aka kwashe kwanaki biyu ana yi a wurare daban-daban a Legas.
A wani labarin kuma, Gwamna Uzodimma Ya Karbi Sabon Kakakin Majalissar Dokokin Imo, Nduka
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya karbi bakuncin sabon kakakin majalisar dokokin jihar, Mista Emeka Nduka, bayan murabus din Mista Kennedy Ibe a ranar Litinin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa ba a bayar da dalilin murabus din Ibe ba.