By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon ministan harkokin waje Farfesa Akinwande Bolaji Akinyemi murnar cikar sa shekaru 80 a duniya a ranar Litinin.
Shugaban, a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya taya masanin, mai gudanarwa, mawallafi da babban jami’in diflomasiyya murna kan wannan mataki.
Buhari ya bi sahun malaman jami’o’i da ‘yan jarida wajen taya tsohon ministan murna, wanda tasirinsa na ilimi da na gudanarwa, ya ce, ya yanke kusan kowane fanni na rayuwar al’ummar kasa, tare da nuna kwarin guiwa wajen tsara manufofi, musamman kan dimokuradiyya, shugabanci nagari da diflomasiyya.
Sannan ya ce Akinyemi ya ci gaba da kasancewa cikin kishin kasa da biyayya ga ci gaban kasa da Afirka, inda ya jagoranci Cibiyar Kula da Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya yana da shekaru 33, ya zama minista yana da shekaru 43, bayan ya samu digirin digirgir a shekaru 27.
Buhari, wanda ya bayyana imanin Akinyemi da hangen nesa,da tsayin daka da kuma kwazonsa ya cancanci a yaba masa, ya yaba da yadda yake son raba gogewa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ciki har da tsara tsarin zabe na dimokuradiyya, da kuma taka rawar gani a tattaunawar duniya da sauran kasashe, Majalisar Dinkin Duniya, Commonwealth, da Tarayyar Afirka.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya da kuma kuzari, musamman wajen nasiha da zaburar da matasa malamai da shugabanni.