Yahaya Bello and Buhari

Buhari Ya Taya Yahaya Bello Murnar Tazarce

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya wato INEC ta ayyana Yahaya Bello na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi.

Yahaya Bello na APC din ya yi nasara ne da kuri’a 406,222.

Sai dai bayan da aka kammala tattara sakamakon, Jami’in zaben ya bukaci wakilan jam’iyyu su sa hannu kan sakamakon na karshe amma wakilin jam’iyyar PDP ya ki sa hannu a sakamakon zaen.

A zaben dai wanda ya gudana a ranar Asabar, kuma aka fara bayyana sakamakon zaben a jiya Lahadi, PDP ta samu kuri’a 189,704 sannan SDP da ta samu kuri’a 9,482.

A wata sanarwa da shugaba Buhari ya fitar ta hannun Kakakinsa ya taya Yahaya Bello murnar sake lashe zaben gwamnan jihar..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *