Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 1.6 domin canjawa shugaban ƙasa motoci, da kayayyakin gyaran su a fadar shugaban ƙasa, a yayinda aka ware Naira Miliyan 650 a matsayin wani kaso na kuɗin aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla a kasafin kuɗi na shekarar 2022.
A cewar Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta Daily Trust, aikin wanda ya ɗauki shekaru da yawa ba’a fara ba, na ɗaya daga cikin ayyuka wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu domin aiwatar wa.
A kasafin kuɗi na shekarar 2022, Ma’aikatar Makamashi nada kasafin kuɗi na Naira Biliyan 301 a shekara mai zuwa, wanda yafi na shekarar da muke ciki ta 2021 wanda ya kasance Naira biliyan 204.
KARANTA WANNAN LABARIN: Filato: Lalong Ya Rantsar Da Zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi 17
A cewar bayanai akan manyan abubuwan dake cikin kasafin kuɗi na shekarar 2022 daga bakin Ministar Kuɗi, Kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki Zainab Ahmed tace aikin wutar lantarkin na daga cikin aikace-aikacen da aka sanya a kasafin kuɗin da aka yiwa laƙabi da “yin aiki domin amfanin nan gaba.
Daga cikin ayyukan da suka tsaya ba’a cigaba ba, aikin wutar lantarki na Mambilla zai samu Naira miliyan 650 a matsayin wani kaso na kuɗin, wannan na zuwane duk da Naira biliyan 10 da aka ware ga aikin a shekaru 6 da suka gabata ba tare da an fara aikin ba.