Buhari ya yaba wa Bankin Masana’antu bisa samar da ayyukan yi sama da miliyan 9
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba wa Bankin Masana’antu, BOI bisa samar da ayyukan yi sama da miliyan tara a cikin shekaru bakwai da su ka gabata.
Ya kuma yaba wa BOI bisa yadda t’ya raba sama da Naira Tiriliyan 1.24 ga ma’aikata miliyan 4.2 da su ka amfana a kanana, matsakaita da manyan masana’antu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta wanke tsohon Manajan NNPC, Andrew Yakubu kan zargin Almundahanar Kuɗaɗe
Shugaban ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya kaddamar dabdogon gini na biyu na BOI, a Abuja yau Alhamis.
Buhari ya ce bankin ya ci gaba da samun nasarar aiwatar da ayyukansa a matsayin cibiyar manufofin gwamnatin tarayya, tare da ba da lamuni mai ƙarancin kuɗin ruwa ga masana’antun.
Don haka ya yabawa mahukuntan ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari da kuma BOI bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen habaka tattalin arzikin kasa da walwalar ‘yan Najeriya.
Comments 1