Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Etsu Nupe Yahaya Abubakar murnar cikarsa shekara 69 a duniya tare da taya shi murna cika shekara 18 a karagar mulkinsa, inda ya bayyana shi a matsayin; ‘mashahurin Sarkin Gargajiya’.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a sakon taya Sarkin murna da Kakakinsa, Malama Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, inda ya bayyana mulkin Abubakar a matsayin jagorancin da ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautarsa.
Shugaba Buhari ya ce; “Etsu Nupe ya yi amfani da basirarsa ta soji wajen aiki tukuru wajen bunkasa zaman lafiya, walwala a tsakanin al’ummarsa”.
“tun bayan nadinka shekaru 18 da suka gabata bayan ka gaji Sanda Ndayako, ka tabbatar da cewa tabbas ka cancanci wannan nadin, saboda, a matsayin na tsohon soja mai ritaya, ina alfahari da ci gaban da kawo wa a karkashin mulkinka ya zuwa yanzu”, inji Buhari.
A cewar shugaban, Sarakunan gargajiya sun fi kusanci da mutane kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Yayin da yake taya Abubakar murnar bukukuwan guda biyu, shugaban ya shawarce shi da kar ya huta a kan dokinsa kuma ya ci gaba da ba da shawara irin ta uba ga shugabanni a dukkan matakai don ciyar da Najeriya gaba.