Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a jiya Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa har kawo yanzu ba a kai ga sanin batun da suka tattauna a tsakaninsu ba, sai dai ana ganin ganawar ta su na da nasaba da batun sasanta rikicinn siyasa da ya ɓarke a ƙasar Mali.
https://dimokuradiyya.com.ng/shugaba-buhari-ya-yi-wata-ganawar-sirri-da-adams-oshiomole/
Goodluck Jonathan dai ɗaya ne daga cikin ‘yan gaba-gaba da ke ƙoƙarin ganin an kawo rikicin siyasa da ya addabi ƙasar ta Mali.
Tun a baya dai shugabannin ƙasashen Afrika da dama sun shiga cikin lamarin rikicin na Mali domin samar da zaman lumana a ƙasar.