Daga Sulaiman Musa
Muhammadu Buhari wanda shine shugaban Nijeriya, ya tofin Allah wadai da wadanda suka sace tare da kashe daliban jami’ar Greenfield a Kaduna.
Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya fitar da jajen Buharin a yau din nan, inda yake mai cewa tabbas ya ji radadin wannan lamarin kuma tunaninsa gaba daya na tare da iyalan mamatan da irin radadi da jimamin da suke ji a cikin ransu.
Buhari ya ce matsalar da ake samu na tsaro tabbas abun damuwa ne, kuma a irin wannan lokacin da ‘yan bindigan suka kashe dalibai, ya nuna cewa tabbas wannan ba abun lamunta bane sam.
Ya ce, za su tabbatar da hukunta ‘yan bindiga masu kashe jama’a babu gaira ko sabab.