Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta’aziyyar shi ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, bayan rasuwar hadimin shi na musamman a fanin yada labarai da hulda da jama’a, wato Alhaji Umar Pariya wanda Allah ya yi wa rasuwa a yau.
Sakon ta’aziyyar wanda hadimin shugaban kasan na musamman fannin yada labarai da hulda da jama’a, Mista Femi Adesina ya saki da yammacin yau talata a birnin Abuja: Inda sakon yak e cewa; Na samu labarin rasuwar hadiminka na musamman, lallai wannan babban rashin ne a gareka.
‘Allah ya baka hakurin rashinshi, Allah y aba iyali, yan uwa da abokan arziki hakuri da juriyyar rashin shi, ina fatan Allah ya gafarta mishi, ya say a huta.