Daga Sulaiman Musa
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta amince da nadin Honorabul Justice Salisu Garba a matsayin mai rikon mukamin babban Alkalin babban kotun birnin tarayya (FCT).
Shugaban majalisar Ahmad Lawan shine wanda ya karanto bukatar Buharin a yayin zaman majalisar na yau.
Babban Alkalin Alkalan Nijeriya (CJN) Hon. Justice Tanko Muhammad, a watan Janairun 2021 ne ya rantsar da Justice Garba a matsayin mai rikon Alkalin Babban Kotun FCT.
Wannan matakin na zuwa ne bayan karewar wa’adin aikin Justice Ishaq Bello na babban kotun FCT da ke Abuja.
Justice Garba wanda ya fito daga garin Malumfashi ta jihar Katsina.
An kira sunansa da Lauya ne a 1984 wanda kuma ya kammala hidimtawa wa kasa NYSC a 1985.
An nada Garba a matsayin alkalin kotun Majistire na FCT a 1989.
Ya zama babban Rijistan babban kotun FCT a 1997. An kuma nada shi Alkalin babban kotun FCT a 1998.