Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya tattauna da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Embalo jim kadan bayan ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki.
Buhari, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya taya Embalo murnar tsira daga yunkurin juyin mulkin, ya kuma yaba wa sojojin da ke biyayya ga kasar Guinea Bissau bisa nuna kishin kasa da ya kai ga nasarar da suka samu kan marasa kishin sojoji.
Ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da kuma mika fatan alheri da goyon bayan gwamnati da al’ummar Najeriya ga gwamnatin Guinea-Bissau da gwamnatin Shugaba Embalo.
Anashi bangaren Shugaba Embalo ya ce an shawo kan lamarin kuma “komai yana nan lafiya, kuma an dawo da doka da oda.”