Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 19.76 a gaban zauren majalisar dokokin kasar a ranar Juma’a.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasa ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kuma aka karanta a zaman zaman majalisar na ranar Talata.
KARANTA ANAN: Kwamitin Amintattu Na PDP Ya Shirya Ganawa Da Wike
A cewar wasikar, za a gabatar da kasafin ne da misalin karfe 10:00 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin gadi.
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce an yi shirye-shiryen karbar dukkan ‘yan majalisar dokokin kasar da kuma tawagar shugaban kasa.
Aminiya ta ruwaito cewa ana gudanar da gyare-gyare a majalisar dattawa da ta wakilai, lamarin da ya sa ‘yan majalisar tarayya suka koma zauren majalisar na wucin gadi.
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Buhari ta kashe ilimi, mu zamu binne shi – NANS
Kungiyar daliban Najeriya NANS shiyyar Kudu-maso-Yamma, ta zargi shugaban kasa Mohammed Buhari da binne ilimi a kasar, inda ta ce a shirye take ta gudanar da jana’izar ta.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan NANS kuma mai magana da yawun hukumar, Adegboye Olatunji da Awoyinfa Opeoluwa, bi da bi, a ranar Litinin.
Kungiyar daliban ta ce za su sake bin titina a cikin kwanaki masu zuwa.