Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zauna da Yan majalisu 109 misalin karfe 8:00 a ranar Talata a Vila. Kamar yadda Jaridar The nation ta wallafa a shafinta
An sanar da lokacin zaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Yan majalisun lokacin da Jagoran Yan majalisu Ahmad Lawan yake Jagorantar zaman Majalisa.
Ade 27 ga watan Aprilu 2021 ne, Yan majalisu suka yanke shawarar sanya lokacin tattaunawa da Muhammadu Buhari don duba yanayin rashin tsaro dake addabar kasar.
KARANTA:- DA DUMINSA: Majalisa ta ki amincewa da nadin Onochi a matsayin Shugabar INEC
Kamar dai yadda sakon gayyatar zaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Yan majalisu ta kasan ce.
“Na rubuto wannan takardar don in sanar da Jagoran Yan majalisu cewar Muhammadu Buhari ya shirya zama tare da Yan majalisu tarayyan Najeriya ranar 13 ga watan July, 2021 da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Talata.”
“Zamu zauna a babban dakin taro na Banquet, a cikin Vila Abuja.”
Cikakken labarin na zuwa………….
A wani labarin Nigeriata gama samun tallafin man fetur da zarar Buhari ya sanyawa dokar PIB hannu
Ministan man fetur ya ce sanya hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari kan dokar PIB zai kawo karshen biyan kudin tallafin man fetur a kasar.
Karamin Ministan Man Fetur Chief Timipre Sylva a ranar Litinin, ya bayyana cewa, Idan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Sanya hannu ga Dokar data Kafa Masana’antar Man Fetur, zai kawo Karshen Kudin Tallafin Man Fetur da Gwamnati ke biya a Najeriya.
Sylva ya sanar da Haka a taron Najeriya da Kungiyoyin Kasashen dake Shigowa da Man Fetur: Shekaru 50 na hadin gwuiwa, a cibiyar Yan Jarida a Abuja.
Yace yafi dacewa ga Najeriya da Gwamnatin Tarayya data daina bayar da Tallafin Man Fetur, yana mai cewa dokar da aka zartar ta PIB babu inda aka sanya bayar da Tallafin Man Fetur.
Ministan ya kara dacewa “Cire Tallafin Man Fetur din nan zai inganta tattalin arzikin Najeriya. Haka yake, kowa nada nashi ra’ayin, Amma ni a nawa ra’ayin, nayi imanin cewa cire Tallafin Man Fetur shine abinda yafi dacewa a Najeriya, bawai Ma’aikata ba.”
“A halin yanzu, tattaunawa da Masu ruwa da tsaki na cigaba da gudana. Amma inaso in sanar daku cewa, Idan Shugaba Buhari ya zartar da Dokar data kafa Masana’antar Man Fetur wato-PIB. Tallafin Man Fetur zai zama doka, domin Yana cikin Dokar PIB cewa Za’a sayar da Man Fetur kamar yadda Kasuwa ta nuna.”
Sylva ya kara dacewa, “cire Tallafin Man Fetur zai zama sanadiyyar Samun Kudaden da za’ayi amfani dasu domin samun cigaba. Abin bakin ciki, barin Tallafin Man Fetur kamar cire hanci ne a fuska.”
Ministan Man Fetur yayi nuni dacewa, Gwamnati zata cigaba da sake Gina Matatun Man Fetur na Warri da Kaduna nan bada jimawa ba, domin inganta tatar Man Fetur a cikin Gida, tare da Magance Matsalolin da Cire Tallafin Man Fetur zai janyo.
Yace hako Danyan Mai na Kungiyar OPEC da aka baiwa Najeriya a watan yuni na Shekarar 2021, a halin yanzu ana hako ganga 1.554 duk rana, Kuma ya taimaka wajen dai-dai ta kudin Man Fetur a Fadin Duniya.