Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar birnin tarayya Abuja a gobe Litinin domin halartar taron kwanaki uku dangane da alakar Rasha da Afrika da zai gudana a birnin Sochi dake kasar Rasha daga ranar 23 ga watan Oktoba zuwa 25.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Lahadi. Inda ya ce taron da shugaban kasar zai halarta zai ba da hankali ne kan bunkasa tsaro, kasuwanci, zuba hannun jari da kuma bangaren kimiyya da fasaha da kuma iskar Gas.
Har wala yau, Kakakin shugaban kasar ya ce; Buhari zai gana da shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin domin karfafa alakar dake tsakanin kasashen.
Daga cikin wadanda za su raka shugaban kasar sun hada da; Gwamna Muhammad Yahaya na Gwambe, da kuma Gwamna Bello Matawalle na Zamfara da kuma Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Ministan harkokin kula da kasar waje, Geoffrey Onyeama, sai kuma Ministan kasuwanci da zuba hannun jari, Adeniyi Adebayo, sai kuma Ministan albarkatun kasa da bunkasa karafa, Olamilekan Adegbite da karaminn ministan man fetur, Timipre Sylva.