Buba Galadima

Buhari Zai Iya Neman Tazarce Karo Na Uku – Buba Galadima

Wani tsohon shakikin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ka da su yi mamaki idan Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi kujerar shugabncin kasa a shekarar 2023.

Galadima, wanda a halin yanzu aboki ne ga Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkshin jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya ce akwai masu ingiza shugaban kasar don ya kara neman zarcewa kujerarsa.

A tattaunawar da ya yi da jaridar The Sun, Galadima ya yi ikirarin cewa, Buhari ya killace ma’aikatar shari’a, a don haka ne ya yi wucewarsa zuwa Saudi Arebiya ana gobe kotun koli za ta duba shari’arsa da Atiku. Kamar yadda ya sanar, “Ban taba ganin mummunan lamari ba kamar abin da muke fuskanta a Nijeriya a yau karkashin jagorancin gwamnatin APC da shugabancin kasar Muhammadu Buhari. Har kuwa lokacin mulkin soji, ‘yan Najeriya ba su taba gurzuwa kamar haka ba”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *