• Buhari Zai Kaddamar da Layin Dogo Daga Kano zuwa Kaduna a yau Alhamis.
• Minista Rotumi Amaechi ne ya bayyana hakan.
• Aikin zai samar da aikinyi ga Yan Naijeriya da kuma farfado da harkokin kin kasuwanci
A yau Alhamis 15 ce,, ake saran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin Layin dogo da zai lakume Dala billiyan 1.2, Wanda da zai tashi daga Kano zuwa Kaduna.
Za’a fara taron kaddamar wanne, a karamar hukumar Dawakin Kudu dake jihar Kano, da musalin Karfe 10 na safen yau.
Aikin Layin dogon, wanda zai hade da layin dogon da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, an Samar da kudaden aikin ne daga Ma’aikatar Sufuri ta kasa.
Tuni dai aka bai wa yan kwangilan da zasu yi aikin na Kamfanin CCECC na kasar China Dala milliyan 218, domin fara aikin, inda daga bisani za’a Basu Dala milliyan 100.
KARANTA WANNAN LABARAN:Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin Yobe ta samu tallafin bunkasa dajin Jakusko Nasari
.
Ministan harkokin sifuri na Kasa Mr Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan, makwanni biyu da su ka gabata. inda ya ce, aikin Layin dogon ba wai harkan sifuri kawai zai inganta ba, inda ya ce, zai farfado da harkokin Kasuwanci tsakanin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, da kuma samar da guraben aiyukan yi ga Yan Naijeriya.
Kana a cewar shi, aikin bagare ne na Layin dogon da zai tashi daga Kano zuwa Maradi, wanda a kasan jihar Kano a matsayin cibiyar kasuwanci.
A wurin taron kaddamar da aikin, a nasa ran wasu manyan jami’an Gwamnati zasu halarci wurin.
Comments 1