Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa Abidjan, babban birnin Ivory Coast don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan kare muhalli musamman yadda za a magance kwararowar hamada.
Sanarwar da fadar shugaban ta fitar, ta ce Buhari zai bar Abuja a yau Lahadi zuwa Abidjan, domin halartar taron na kwana biyu da za a soma a ranar Litinin.
Taron ya shafi yadda za a magance kwararowar hamada da fari da zabtarwar ƙasa da sauran matsalolin muhalli, wanda zai ƙunshi shugabannin ƙasashe da sauran masu ruwa da tsaki.
Buhari zai tafi tare da rakiyar muƙarraban gwamnatinsa da suka ƙunshi ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da na muhalli Mohammed H. Abdullahi da ministan noma Dr Mahmoud Mohammed da kuma na ruwa Inginiya Suleiman H. Adamu.
Mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwa da ya rabata ga manema labarai a yau Lahadi.