By Ishaq Dabai
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira ma’aikatan lafiya masu neman kwarewa NARD dasu koma bakin aikinsu dan cigaba da duba marasa lafya.
Buhari yayi wannan kirane yayin gudanar da tattaunawa da kungiyar likitoci ta kasa NMA a gidan gwamnati dake Abuja.
Shugaban ya bukaci da sauran wadanda suke yajin aikin da suke na tsawon wasu watanni da suka shafe suna yi biyo bayan bukatar da suke nema a wajen gwamnatin tarayya na albashinsu da suke bi.
Bashin da ma’aikatan lafiya suke bin gwamnatin an dai daita komai hakan ya fitone ta bakin mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu yace “gwamnati ta tattara dukkanin baya nai na biyan kudin da suke bin gwamnatin bashi, da fenshon da kuma ‘yan kwangila da sauran bashi da suke bin gwamnati a baya sun rigaya sun biya kuma suna da tabbaci.
Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire shima ya samu halattar zaman tattaunawa yace kungiyar ta NMA wasa sukeyi akan cigaban harkar lafiya musamman dakile annoba kan manufofin su da lafiyar al’umma.