Dan wasan gefe na Arsenal Bukayo Saka ka iya sha’awar komawa Liverpool, a cewar wani rahoto.
Dan wasan mai shekaru 20 da ya kammala karatun digiri ya inganta wasansa zuwa sabon matsayi a karkashin Mikel Arteta kuma yana jin dadin kakar wasa na bana, inda ya zira kwallaye shida tare da bayar da taimako hudu a wasanni 21 a duk gasa da ya buga.
Ana kyautata zaton Arsenal na son bai wa Saka sabon kwantiragi, inda wani rahoto ya ce yarjejeniyar shekaru shida tana kan teburi domin neman amincewar Dan wasan.
Koyaya, Podcast Window ya ba da rahoton cewa dan wasan na Ingila da wakilansa suna ‘sha’awar ya koma Kungiyar kwallao kafa ta Liverpool.
An fahimci Jurgen Klopp yana neman masu maye gurbinbyan wasansa kamar Mohamed Salah, Sadio Mane da Roberto Firmino, wadanda za su kai shekaru 30 a farkon kakar wasa mai zuwa.
Saka, wanda yake kwantiraginsa a filin wasa na Emirates har zuwa watan Yunin shekarar 2024, ya buga wasanni 109 a dukkan gasa da Gunners, tun lokacin da ya fara buga wasa a watan Nuwamban Shekarar 2018, inda ya zura kwallaye 17 sannan ya taimaka aka ci 25.