Hukumar tsaro ta NSCDC, a Kaduna ta ce za ta raba jami’anta 2, 500 a fadin jihar domin su taimaka wajen tabbatar da tsaro a yayin bukin Kirsimeti.
Kwamandan NSCDC din, Nurradeen Abdullahi a jihar Kaduna, shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake yi wa shugabannin sashe na hukumar tsaron bayani a ranar Talata a Kaduna.
Abdullahi ya ce raba jami’an ya zama wajibi domin tabbatar da an fara bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara lafiya an kuma kare lafiya.