Daga Idris Zariya
A ci gaba da bayar da tallafi da kungiyoyi masu zaman kansu ke gudanarwa don taimakon kai da kai musamman kasantuwar halin da Jama’a ke ciki sakamakon ballewar annobar cutar korona a wannan lokacin wadda hakan ya jefa rayuwar Jama’a cikin mawuyacin hali da kowa ke fatan Allah ya kawo karshen lamarin gida da waje.
Bisa ga wannan ne, kungiyar Mata musulmai dake harabar Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da ake kiran su da ‘Muslims Forum’ suka shirya bayar da tallafi ga mutum akalla 253 ga masu karamin karfi a karkashin jagorancin Hajiya Binta Aminu Dorayi.
Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka shaida yadda lamarin ya gudana. Kungiyar matan sun yi amfani da ranar 30 ga watan Yulin 2020, wanda ranar ta yi daidai da ranar jajiberin babbabar sallah don bayar da tallafin ga mabukata.
Kuma sun gudanar da bayar da tallafin ne a harabar Jami’ar ta Ahmadu Bello Zariya a sashen kula da lafiyar Dabbobi wato (Vet medicine).
Bayan da suka kammala bayar da tallafin ne sai wakilan kafafen yada labarai suka nemi jin ta Bakin Amirar kungiyar Hajiya Binta Aminu Dorayi akan bayar da tallafin.
Hajiya Binta Aminu Dorayi ta bayyana dalilinsu na bayar da wannan tallafi ga mutane 253 inda ta ce, sun yi hakan ne don neman yardar Allah madaukakin sarki. Kuma ta kara da cewa; tarihi ya nuna cewa duk wanda ya ciyar da wani a cikin goman karshe wannan watan mai alfarma, to Allah zai albarkacin komai nasa, ta ce hakan ya sa muka yi shawarar da sauran ‘ya’yan kungiyar da su fito su bayar da tallafi a wannan lokacin kuma jama’a sun bayar da goyan baya sosai tunda gashi har sun sami damar sayo shanu guda biyu da buhunan shinkafa masu yawa don bayar da tallafin don haka ta godewa Allah tare da sauran mutane da suka bayar da gudummawarsu.
A karshe shugabar ABU Muslims Forum ta tabbatar da cewa kungiyar ta su ba a nan ta tsaya ba, lokaci bayan lokaci sukan ziyarci gidan Marayu don bayar da gudummawarsu, kuma suna kokari a yanzu haka domin su siya babban fili don yin makarbartar Musulmi a wata anguwa da ake kira Mil goma dake daura da Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.
Ta ce duk da taro da sisin da suke tarawa ne suke gudanar da wannan hidima don haka ta ce hanya a bude take don bayar da gudummawar ga kowa mai son ci gaban addini don taimakawa addinin Allah.
Ita dai Hajiya Binta tana aiki ne a asibitin dake harabar Jami’ar a bangaren magani wato Pharmacy. Kuma ta Sami yabo a bangarori da dama wajen taimako al’ummar da take tare da su.
Malama Ramatu Garba na daya daga cikin wadanda suka sami tallafin kayan masarufin don bikin sallah, ita ma ta nuna jindadinta tare da fatan alheri ga ABU Muslims Forum.