Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya soki batun rufe majalisar dokokin jihar Filato kan rikicin shugabanci.
Rufewar ya biyo bayan tsige Ayuba Abok a matsayin shugaban majalisar da ‘yan majalisa takwas suka yi a ranar 27 ga watan Oktoba, wadanda suka zabi Yakubu Sanda a matsayin sabon shugaban majalisar.
DUBA WANNAN LABARIN: Osibanjo ya Bayyana hanyoyin dakile Ƙaura tsakanin kasashe ba bisa ƙa’ida ba
Bangarorin biyu sun ci gaba da yin ikirari ga shugabancin majalisar, wanda kuma magoya bayan su ke cigaba da haifar da tarzoma.
Saraki, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu ya fitar, ya bayyana rufe Majalisar a matsayin wani abu kaico da kuma yin amfani da martanin da bai dace ba don gyara wani abin da bai dace ba.
Ya ce rufe majalisar zai hana jama’a samun wakilci da kuma hana majalisar yin aikin da aka zabo mambobinta domin su gudanar.
Comments 1